Jerin wasu ‘yan sama jannati na ci gaba da kokarin sauya tsofaffin baturan wasu na’urorin mutunmutumi da aka aikesu duniyar sararrin samaniya ta kasa-da-kasa don wani bincike.
Dan sama jannati Christina Koch da Andrew Morgan sun samu nasarar cire baturan na’urorin uku, da kuma samun nasarar saka sabbin baturan biyu ga mutunmutumin. Ana dai inganta baturan da karfin da basu bukatar sai an sakawa kowanne guda biyu, batiri daya ya wadatar.
“Nasara ta samu a aikinmu na yau” a cewar Koch, yau babbar rana ce don kuwa wannan wani jan aiki ne, amma tunda mun iya samun nasarar canza biyu ai sai muyi godiya ga Allah. Ana dai sa ran Koch da Morgan su kara gaba cikin duniyar sama a ranar Juma’a , tafiyar da ta kai nisan kilomita 400 don canza sauran batura a wasu na’urorin.
Kowane batiri daya na da nauyin kilogiram 800 girman shi kuwa ya kai girman firij, ‘yan sama jannatin dai sun fara wannan aikin na inganta baturan ne tun a shekarar 2017, wanda ya zuwa yanzu sunyi rabin aikin.