‘yan Republican sun amince da jerin manufofin da jam’iyyarsu zata yi yakin neman zabe a kai

Wakilai a zauren taron jam'iyar Republican

'Yan Republican sun amince da jerin manufofin da jam’iyyarsu zata yi yaki neman zabe a kai a wajen babban taron da suke yi a Tampa, wadanda suka kunshi haramta zub da ciki da auren ‘yan luwadi, tare da kin yarda da matakin yin amfani da kudaden gwamnatin tarayya wajen farfado da tattalin arziki da samar da karin ayyukan yi.

Har ila yau jerin manufofin sun ce ‘yan ‘yan Republican a majalisar dokoki sun kuduri aniyar soke shirin inganta kiwon lafiya na shugaba Obama, wanda aka fi sani da suna Obamacare, tare da fadin cewa shugaba dan Republican zai ja burki ga aiwatar da shirin, ya kuma sanya hannu kan dokar soke shi idan ya zo gabansa.

Manufar ta Republican zata takali koma-bayan tattalin arziki mafi muni da aka gani tun wargajewar tattalin arziki na shekarun 1929 zuwa farko-farkon shekarun 1940, ta hanyar sauya tsarin haraji don taimakawa kananan kamfanoni da ci gaba da aiki da shirin rage haraji na shugaba Bush.

Har ila yau, jerin manufofin sun amince da ikon da jihohi da gwamnatin tarayya suke da shi na kin yarda da auren jinsi guda.