'Yan Republican Na Fargaban Nasarar Hillary Clinton A Zaben Shugaban Kasa

Matar Shugaban kasar Amurka Michelle Obama da Hillary Clinton

A takarar majalisu a Amurka, Yan jam’iyyar Republican sun fara bayyana fargabarsu akan Demokrats domin Hillary Clinton zata zama shugabar kasa.

Kasan cewar Donald Trump yana samun koma baya a kuri’ar neman ra’ayi ta kasa baki daya, Yan jam’iyyar Republicans da suke takarar majalisa sun yi kira ga masu zabe da su zabe su a karkashin takardar da suka zabi Clinton a matsayin shugaban kasa. A yayinda su kuma Yan Jam’iyyar Democrats suke cewa Clinton tana bukatar abokanai da zata hada kai da su a majalisa don aiwatar da burinta

A zazzafar takarar majalisa da ake bugawa a jihar Minnesota, Stewart Mills dan jam’yyar Republican ya saduda da dan takarar shugabancin kasa. Yace Donald Trump na jam’iyyarsa ba zaiyi nasara ba a ranar 8 ga watan Nuwamba, amma yayi kokarin yin amfani da wannan damar a tallan kemfen da yayi a talabijin dangane da abokin hamayyarsa na Demokrat Rick Nolan, yana kiran masu jefa kuri’a su zabeshi, wato suyi watsi da Rick Nolan din.