A yayin da ya rage saura kwanaki uku a gudanar da babban zaben shugaban kasa dana majalisar dokoki a jamhuriyar Nijer, haka 'yan kasar mazauna Kamaru ke ci gaba da yin cin cirindo a kofar ofisoshin kananan jakadun su domin shirye shiyen kada kuri'un su kamar yadda dokar kasar Nijer ta tanada.
Wani tsari na dokar kasar jamhuriyar Nijer da ya banbanta ta da sauran kasashe kamar Najeriya shine, 'yan kasar na iya kada kuri'un su daga wata kasa, ba lallai dole sai suna cikin kasar ta Nijer ba.
Ta dalilin haka ne matasa da magidanta dake zama a kasar ta Kamaru suka tashi tsaye wajan karbar katunan zabe dakuma bayyana ra'ayoyin su dangane da irin manufofin jam'iyyun kasar.
Wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Mahamud Auwal Garba ya sami zantawa da wasu matasa da magidanta 'yan Nijer mazauna jamhuriyar Kamaru a yayin da suke kan karbar katunan zaben kuma sun yi kira ga daukacin 'yan kasar da su gudanar da zaben cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ga cikakken rahoton;