Tunda mahukumtan Najeriya suka shawarar gina layin dogo daga Fatakwal zuwa birnin Konni a jamhuriyar Nijar kan kudi Naira milyan dubu goma sha biyar (Bilyan 15) 'yan kasar Nijar suke ta nuna farin cikinsu.
A cewar 'yan Nijar tsohon mafarki ne ya tabbata saboda a lokacin yakin neman shugaban kasa, Mahammadou Issoufou, ya yi masu alkawarin jawo masu layin dogo daga Najeriya har zuwa tsakiyar garin Konni inda za'a kafa tashar daukan fasinja.
Alhaji Mai Fada shi ko cewa ya yi, suna fatan ganin zuwan layin-dogo a cikin Nijar, musamman a birnin Konni inda nan layin zai fara shiga kafin zuwa wasu wuraren. Yana fata a yi aikin domin ci gaban al'umma. Ya kara da cewa a yi kokari a taimaki matasa su samu abun yi domin a rage zaman banza. Idan ba'a yi hakan ba, ana iya soma samun wasu sace-sace da rashin zaman lafiya.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5