Jiya lahadi al'ummar Jamhuriyar Nijar suka jefa kuri'a a kan sabon tsarin mulki wanda zai maye gurbin wanda hambararren shugaba Mamadou Tandja ya zartas.
A lokacin da ya ke jefa kuri'arsa a Yamai, babban birnin kasar, shugaban gwamnatin mulkin sojan da ta hambarar da Tandja a watan Fabrairu, Janar Salou Djibo, ya bayyana ranar ta lahadi a zaman "muhimmiya."
Tandja ya zartas da tsarin mulkin da ya ba shi karin iko, ya kuma kara masa wa'adi a kan karagar mulkin kasar.
Sabon tsarin mulkin da aka jefa kuri'a a kai jiya lahadi, zai maido da ka'idar yawan wa'adin da shugaban kasa zai iya yi kan mulki, tare da rage irin ikon da shugaban yake da shi.
Sojoji sun yi alkwarin maido da mulkin farar hula a Nijar. Idan har aka amince da sabon tsarin mulkin, za a share hanyar gudanar da zabubbuka na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki ke nan a watan Janairu.
Juyin mulkin watan Fabrairu shi ne na hudu da aka yi a Jamhuriyar Nijar tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960. A farkon watan Oktoba gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta ce ta murkushe wata makarkashiyar juyin mulkin da wasu hafsoshi suka kulla, sun kuma kama wasu manyan hafsoshi hudu.