Yawancin wadanda Muryar Amurka ta magana da su akan wannan batun sun nuna cewa idan Bera da sata to daddawa na da wari, domin yawancin yan Najeriya ba sa son biyan haraji, kuma wanan kari ne da zai taimakawa mahukuntan kasa da talakawan baki daya.
Hajiya Mariya Ibrahim Baba na cikin masu irin wanan ra'ayin saboda haka tana goyon baya, kuma ta kalubalanci gwamnati da ta dage wajen wayar da kan al'umma akan muhimmancin biyan haraji idan har ana so a ci gaba.
Shi ma Sa'idu Yaro Tafawa daga karamar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, ya bi tarihi ne tun daga karin kudin Man Fetur daga Naira 65 zuwa Naira 143, ya zuwa rufe iyaka da shugaban kasa ya ce a yi, inda ya koka cewa talaka ne ke wahala, kuma yanzu aka kara haraji. haka kuma ya fito ya kalubalanci yan Majalisa da fadar shugaban kasa cewa, shi bai goyi bayan karin ba saboda akan talakawa yake karewa..
Shi kuwa tsohon dan Majalisar Wakilai Ahmed Aliyu Wadada ya ce ya kamata a hada hannu da manyan masu kudi wajen kawowa talaka sauki, amma tunda biyan haraji zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasa, sai al'umma su yi hakuri domin Majalisa ta riga ta amince da shi.
Amma daya cikin yan Majalisar Dattawan da suka amince da kudurin karin haraji Sanata Kabiru Gaya ya ce karbar wanan haraji ba zai shafi talaka ba ko kadan, kuma kudaden da za a samu, sune za su shiga lalitar gwamnati a rika rabawa Jihohi da kananan hukumomi, kuma zai hana a ci bashi domin aiwatar da kasafin kudin kasa.
Wanan karin Harajin dai ba za a fara shi ba sai a watan Fabrairu na shekara 2020 saboda haka yan kasa sun zuba ido su ga irin matakin da yan kasuwa za su dauka.