ZABEN2015: ‘Yan Najeriya Su Zabi Wadanda Suka San Halinsu

Na'urar tantance katin zabe

Wani mafashi bakin siyasa daga Bauchi yace kar 'yan Najeriya su sake zabar 'yan takarar da ba su san halinsu a cikin al'umma ba tunda kullum tare suke da masu neman mukamen tun kafin su fara neman mukamai.

Zaben gwamnoni da za’a yi gobe asabar a Najeriya sai mutanen kasar sun lura da ko su wanene ‘yan takararsu, domin kuwa ko ba komai a kalla masu neman mukaman gwamna ko majalisar jiha sun haura shekaru arba’in a duniya.

Idan kuwa sun kai arba’in da haihuwa to mutanen yankinsa sun san ko shi wanene in na gari ne ko sabanin hakan. Inji wani mai fashin baki a hirar da Mahmud Lalo na Muryar Amurka yayi da shi.

Mai duban al’amuran yau da kullum kuma Malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Jihar Bauchi cewa yayi Abubakar Sufyan yace kowa ya bude idonsa kar a yaudari jama’a da fakewa da canza sheka daga nan zuwa can.

Ya kuma nuna cewa a bi a hankali wasun su akwai rade-radin wasu na canza sheka ne kawai don neman mukamai idan mulkin ya tabbata a hannun jam’iyyar ta APC.

Game da maganar canjin sheka bayan faduwa zabe yace ba dabara bace. Ya kamata idan mutum ya fadi ya koma ya sake shiri ta hanyar yin nazarin abinda ya kada shi a zaben don ya tari gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN2015: ‘Yan Najeriya Su zabi Wadanda Suka San Halinsu-5'11"