‘Yan Najeriya Naci Gaba Da Bayyana Ra’ayin Su Game Da Dawowar Shugaba Buhari.

  • Ladan Ayawa

Dawowar Shugaba Mohammadu Buhari Daga Birnin London

'yan Najeriya naci gaba da bayyana raayoyin su game da dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga kasar Birtaniya bayan ya kwashe sama dakwanaki 100 yana jinya

Ranar Juma’a shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya tafi jinya kasar Birtaniya ya koma gida bayan kwashe sama da kwanaki dari.

Wannann yasa ‘yan kasar keci gaba da bayyana raayoyin su game da wannan tafiyar.

Wakilin sashen Hausa Hassan Umar Tambuwal da ya zaga cikin babban birnin jihar Oyo, Badun ya jiwo raayoyin wasu ‘yan Najeriya.

Da farko Manuga Dan jam’iyar PDP dake zaune a unguwar karan shanu a birnin na Badun yace yana wa shugaban marhabin kuma yana fatar ALLAH ya kara masa lafiya. Sai dai kuma ya nemi shugaban da kar ya manta da alkawurran da yayi wa ‘yan Najeriya musammam akan batun gyaran hasken wutan lantarki.

Shiko Mohammed Umar ya shaidawa Hassan cewa ne yayi murnan dawo war shugaba Buhari musammam irin abubuwan da yayi wa kasa kafin tafiyar sa, irin tsaro da ya samar a jihar Borno musamam a yankin su na Baga.

Ga Hassan Umaru Tambuwal da sauran Raayoyin Jamaa 2’42

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Najeriya Naci Gaba Da Bayyana Ra’ayin Su Game Da Dawowar Shugaba Buhari.2'42