‘Yan Najeriya Na Zanga-zanga Saboda Masu Garkuwa Da Mutane Sun Addabe Su

Your browser doesn’t support HTML5

Mazauna birnin Damishi a Najeriya sun bazama akan tituna a ranar Alhamis don gudanar da zanga-zanga kan yadda suke fama da matsalar tsaro da yawan garkuwa da mutane da ake yi a Kaduna da ke arewacin kasar.

Dan karamin gangamin masu zanga-zangar sun sun rufe kan hanya suna rera wakokin neman a kai masu dauki don sus amu zaman lafiya.

Daya daga cikin masu boren ya ce akalla mutum 16 aka yi garkuwa da su a ‘yan kwanakin nan.

Fitar masu zanga-zangar na zuwa ne kwana biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka far wa wata makaranta suka sace dalibai 121.