‘Yan Najeriya Na Kokawa Kan Hauhawar Farashin Kayan Masarufi Yayin COVID-19

Wata yarinya a kasuwar Obalende da ke Legas

Wata yarinya a kasuwar Obalende da ke Legas

A daidai lokacin da wasu yan Najeriya ke cigaba da kokawa a kan yanayin kuncin rayuwa sakamakon annobar coronavirus, hauhawar farashi musamman a kayayyakin masarufi a kasar na dada sanya mara sa karfi a wani hali.

"Wannan rashin adalcin yan kasuwa ne ba na gwamnati ba saboda su suke kara farashin abubuwa."

Zainab Isma’il dake sana’ar sayar da abinci a unguwar Jabi na babban birnin tarayyar Najeriya kenan da ra’ayin ta a kan tashin farashin kayayyakin masarufi a kasuwa.

Shi ma Muhammad Abdulkarim Saleh, wani mai gyaran waya a unguwar GSM village ya bayyana wa Muryar Amurka yadda batun hauhawar farashin kayayyaki ke kawo musu cikas a yayin ayyukansu.

"Kafin coronavirus zaka iya siyan screen din waya a kan dubu goma, a yanzu ba zaka samu kombi kasa da dubu ashirin ba."

Masanin tattlin arziki a kasar, Kasim Garba Kurfi, ya danganta batun hauhawar farashin kayayyaki da "bambancin da gwamnati ke sawa kan farashin canjin kudi tsakaninsu da 'yan kasar."

Hauhawar farashin kayayyaki dai ya kara tsananta ne tun bayan rufe kan iyakokin kasar da gwamnati ta yi a watan Augustar shekarar 2019 da kasashe makwabta saboda yaki da ayyukan shigowa da shinkafa irin na waje domin bunkasa aikin noma a Najeriya

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu daga kaso 12.3 cikin 100 a watan Afrilu zuwa kaso 12.4 a watan Mayun lamarin da ya yi sanadiyar kari a kan kayayyakin masarufi, ayyukan sufuri, magunguna da kayayyakin asibiti a kasar.

Hauhawar farashin kayayyakin masarufi kadai ya kai kimanin kaso 60 cikin 100 lamarin da wasu masana tattalin arziki suka daura alhakin hakan a kan ayyukan ‘yan bindiga, rashin karfin gwiwa daga bangaren masu zuba jari, tare da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya sakamakon annobar Coronavirus duba da yadda Najeriya ta dogara kacokan ga bangaren albarkatun man fetur.