Da ya ke bayyana ra’ayinsa game da batun, kwararre akan sha’anin tattalin arziki Shu’aibu Idris Miqati, ya ce duba da tarihin matatun man Najeriya, a yanzu a wannan karnin a ce za a dauki kudi a narka a matatun man da sun kai kusan shekaru 40 da aka gina su kuskure ne, saboda yanayin kimiyar sarrafa mai na zamani ya canza da irin ijinan da matatun mai ke dasu. Bayan haka, an sha gyara matatun nan a baya amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Ya kara da cewa, badakalar cin hanci da rashawa, cin amana da suka yi katutu a kasar zasu sa aikin ya zama da wahala saboda kason kudin da aka ware da yawa wasu ne zasu wawuresu.
Karin bayani akan: Shu’aibu Mungadi, Fatakwal, Nigeria, da Najeriya.
Shi ma malam Shu’aibu Mungadi, mai sharhi kan lamuran yau da kullum, cewa ya yi zarge-zargen cin hanci da rashawa sun yi yawa a jami’an gwamnatin Najeriya, idan aka duba za a ga hakan ya faru a bangaren wutar lantarki na kasar. Gwamnati ta kashe kudi da yawa don a gyara bangaren kafin a saida wa ‘yan kasuwa amma duk da haka ana ci gaba da kashe kudi a wannan bangaren.
Ya kara da cewa, inda ma a ce bayan kashe wadannan makudan kudaden za a samu saukin matsalar man fetur a Najeriya kuma za a hana shigo da man, to da babu damuwa, domin shigo da mai ne ya durkusar da tattalin arzikin Najeriya. Idan har da gaske gwamnati ta ke, a cewar Mungadi, to ko dai a saida matatun, ko kuma a gina sabbi. Amma ba zai yiwu a yi amfani da matatun a matsayin wata kafa ta sace kudaden Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5