'Yan Najeriya Mazauna Nijar Sun Yi Tsokaci Akan Kasafin Kudin Wannan Shekara

Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya da Shugaba Issoufou Mahammadou na Jamhuriyar Nijar

Kwana guda bayan da majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da sabon kasafin kudin kasar da ya fi Naira tiriliyon bakawai 'yan kasar dake zaune a Jamhuriyar Nijar sun tofa albarkacin bakinsu

Kasasfin kudin ya bayyana irin ayyukan da gwamnatin zata yiwa 'yan kasar cikin wannan shekarar da ta kusa kai rabi.

'Yan Najeriya dake zaune a kasashen waje ne suka soma tofa albarkacin bakinsu tare da son sanin makomarsu a cikin wannan sabon kasafin. Musamman suna son su san irin tanadin da aka yi masu, wato irin su dake kasashen waje.

Timothy wani dan Najeriya dake zaune a Jamhuriyar Nijar yace sun ji dadi amma yakamata a tuna da su da suke waje domin su ma a yi masu taimakon da ya dace. Yayi fatan Allah ya sa kasafin ya zama alheri ga kowa.

'Yan Najeriyan dake waje suna nuna fata nagari tare da cika alkawarin da hukumomin tarayyar kasar su kayi. Sun zayyana irin ayyukan da suke son su ga kasafin ya cimma domin cigaban Najeriya.

Wani Abubakar dan jihar Kebbi yace sun dade suna jira su ji 'yan majalisar kasar sun amince da kasafin kudin. Injishi dama Shugaba Buhari yana son ya yiwa talakawa aiki ne. Ya roki Allah ya taimakeshi aiwatar da ayyukan alheri.

Wani kuma cewa yayi a kara taimakawa ayyukan noma kamar yadda shugaban kasa yace ya maida hankali akan habaka noma. Saboda haka a taimaka da takin zamani cikin lokaci.

Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Najeriya Mazauna Nijar Sn Yi tsokaci Akan Kasafin Kudin Kasarsu Na Wannan Shekara - 3' 02"