Wani babban jami’in hukumar dake yaki da fataucin mutane ta Najeriya ko NAPTIP a takaice, Mr. Josiah Emeron ya shaidawa Muryar Amurka cewa jirgin ruwan yakin kasar Andalusa ya kai taimako ga jirgin ruwan dake kan hanyarsa zuwa Turai wanda ya makale a tekun Bahar Rum inda ‘yan mata su 26 daga Najeriya suka rasa rayukansu.
Jami’in yace lamarin abun bakin ciki ne garesu a matsayinsu na hukumar dake kokarin hana mutane bi ta kasar Libya suna neman tsallakawa zuwa Turai ta tekun Bahar Rum. Ya ce duk da kokarinsu wasu sun yi kunnen kasha, suna bi ta barauniyar hanyar.
Hukumar yaki da fataucin mutane ta Najeriya ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da cikakken bincike akan yadda ‘yan Najeriya ke mutuwa akan hanyar haramtacciyar bulaguro. Ya ce mace macen sun yi yawa akan tekun Bahar Rum kuma tamkar ana kashesu ne da gangan, musamman a kasar Libya.
Hassan Maina Kaina na da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5