Mannan matsalar ta sa mata da dama rasa mazajensu, inda hakan ya haifar da dubban marayu. Gwamnatocin da wannan ibtila'in ya shafa sun kai ziyara wadannan wurare don sannin halin da mutane suke ciki.
WASHINGTON DC —
'Yan Najeriya sama da dubu dari da ishirin ne su ka yi hijira zuwa Niger daga Najeriya, sakamakon rikicin 'yan kungiyar Boko Haram da ya addabi yankin sama da shekaru goma. Wannan adadi wani kaso ne cikin 'yan gudun hijirar da ke neman mafaka a kasashen Niger, Kamaru da Chadi. Wadannan kasashe suna da al'adu da suke kamanceceniya da al'adun Najeriya, dalilin da ya bai wa 'yan gudun hijirar kwarin gwiwar ci gaba da neman mafaka a wadanan kasashe.
'Yan gudun hijiran sun rungumi sana'o'i dabam-dabam domin taimaka wa kansu iya gwargwado.
A saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5