‘Yan Najeriya Da Aka Dawo Da Su Sun Ce Sun Azabtu A Libiya

  • Ibrahim Garba

Wasu bakin haure na marmarin barin Libiya

"Kowa ya bar gida, gida ya bar shi." Wannan karin magana, ga dukkan alamu, 'yan Najeriya da su ka makale a Libiya, sun ga sahihancinsa a zahirance saboda sun yi gudun gara ne su ka hau zago, ganin yadda aka rika kirba su tare kuma da azbtar da su tamkar bayi. Tuni wasunsu ke cewa ashe gwamma.

Wasu daga cikin ‘yan Najeriya 130 da aka dawo da su daga kasar Libiya sun ce an kasa masu aya a hannu a kasar da yaki ya daidaita. Hukumar Kula Da Kaurar Jama’a Ta Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ne su ka dawo da ‘yan Najeriyan. Wadanda aka dawo da su din sun hada da maza casa’in da bakwai da mata talatin da tara da kuma kananan yara talatin da takwas.

Mr Joseph Somake, babban shugaban Hukumar Yaki Da Safarar Bil’adama shiyyar Lagos ya ce ‘yan Najeriya da aka dawo da su akasari daga kasar Libiya a wannan shekarar kawai sun kai sama da dubu biyar da dari shida. Y ace akwai ma wasu da su ka dawo daga kasar Gabon da kuma kasar Burkina Faso.

Wakilin Sashin Hausa a Lagos Babangida Jibrin y ace akasarin wadanda ke yinkurin tafiya kasashen Turai ‘yan kudancin Najeriya ne imbanda abin da ba a rasa ba. Alal misali Babangida ya gamu da wani dan jahar Borno mai suna Idris mai sana’ar fentin gidaje a Libiya, wanda aka kama shi aka kuma jefa shi kurkukuku. Wata ‘yar kabilar Ibo mai suna Chioma Eze ta ce kowace rana sai an mata sun sha bulala a Libiya.

Ga wakilinmu Babangida Jibrin da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Najeriya Da Aka Dawo Da Su Sun Ce Sun Azabtu A Libiya