‘Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana alhini kan tagwayen hare haren kunar bakin waken da aka kai a birnin Kaduna, wanda bisa ga dukan alamu an kai ne da nufin hallaka fitaccen limamin nan shugaban kungiyar Izala Sheikh Dahiru Bauchi da kuma tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyar hamayya ta APC Janar Muhammadu Buhari.
Hare haren dai sun yi sanadin mutuwar kimanin mutane ssama da tamanin suka rasu da kuma raunata wadansu da dama, sai dai wadanda aka tsinkaya da harin duka sun tsallake rijiya da baya.
Mutanen da Muryar Amurka tayi hira da su , sun bayyana takaici ganin yadda gwamnati ta gaza shawo kan matsalar. A cikin bayanansu, sun bayyana yadda gwamnati take kashe makudan kudi da sunan ayyukan tsaro amma lamarin yana kara muni kowacce rana.
Yayinda wadansu suke ganin gazawar gwamnati wadansu kuma suna danganta wadannan hare hare da siyasa.
Ga ra’ayoyin da wakilinmu na shiyar Bauchi Abdul’wahab Mohammed ya aiko mana.
Your browser doesn’t support HTML5