Wannan batu na shugaban kasa dai ya sake tayar da wata sabuwar muhawara, yayin da wasu ke ganin cewa wani abune mai wuyar gaske ace an sake samun wayannan mata kamar yadda suke, wasu kuma na cigaba da kyautata zato ne na cewa akwai yiwuwar sake gano wadannan ‘yan mata. Ko a makonni biyu da suka gabata ma sai da shugaban ya tura gwamnan jihar Borno Hon Kashim Shettima, don ganawa da iyayen matan na garin Chibok, inda ya shaida musu cewa nan bada dadewa ba gwamnati zata dawo musu da ‘ya ‘yan su.
Sanata Mohammed Ali Ddume ‘dan majalisa ne mai wakiltar mazabar kudancin Borno, wanda garin Chibok din ya zamanto karkashin sa bayyana ra’ayin sa kan wannan batu, inda yake ganin yanzu an sami shugaba da yake da gaske wajen ganin an samo ‘yan matan.
Wasu kuma iyayen ‘yan matan da aka sace sunce haryanzu dai suna jiran ‘ya ‘yan su kamar yadda shugaba yayi alkawarin za’a nemo su, suna kuma rokon Allah da yasa alkawarin da yayi na samo wadannan yara ya cika shi. Wasu iyayen kuma na fatan wannan alkawarin ba zai zamanto irin na shugabannin baya bane.
Wannan batu na ‘yan matan Chibok dai wani abune da duniya bazata manta ba, ganin yadda wadannan mahara suka kwashe yaran cikin dare ‘daya, kuma har ya zuwa rana mai kamar ta yau babu su babu duriyarsu, illa wadanda suka sami kubucewa tun a wancan lokacin.
Saurari rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5