'Yan-Mata A Sudan Sun Fara Shiga Gasar Lig

Kasar Sudan ta Arewa dake gabashin Afirka, a karon farko ta fara wasan lig na kwallon kafar mata a birnin Khartoum.

Hakan wani abu ne da ba a taba tunanin yiwuwarsa ba a zamanin mulkin tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir, musamman bayan da kasar ta
koma tafarkin Shari'ar Musulunci, a shekarar dubu daya da dari tara da tamanin da Uku.

Cikin wadanda suka kalli wasan harda Mervat Hussein, wacce ita ce shugabar kula da kwallon kafa ta Sudan, wasan da ya gudana a ranar Litinin bayan tashi wasan ta shaida wa manema labarai cewa "wannan babbar dama ce da aka ba Mata a bangaren kwallon kafa.

Ta kara da cewa 'yan wasa da dama sun dade suna jiran wannan lokacin, kuma babbar dama ce a garesu.