'Yan majalisan sun kare matakin da suka dauka na karawa kansu kudi amma 'yan Najeriya na ganin basu yi la'akari da halin ya-ni-yasu da tattalin arzikin kasar ke ciki ba tare da halin kunci da yawancin 'yan Najeriya suka fada ciki.
Bayanin da 'yan majalisun suka fitar ya nuna cewa zasu kashe N6.4bn wajen sayen motoci na alfarma yayin da za'a kashewa motocin kudin sayen mai har na N270.974m. Za'a yiwa motocin inshora na N1.6bn.
Su 'yan majalisun kuma zasu kashewa kansu N11.5b wajen yawace yawace a ciki da wajen Najeriya.
Dangane da wannan kasafin kudi da 'yan majalisun suka amince dashi Muhammad Murtala Yusuf Tama mazaunin Legas yace hakika yayi fatan Allah ya sa 'yan kasar na birni da kauye su anfana dashi.
Masana tattalin arziki sun yi tsokaci akan kasafin kudin. Dr. Dauda Muhammad Kontagora dake Jami'ar Bayero a Kano yace zai yi tasiri saboda ya zama doka kuma zai ba gwamnati damar yin ayyukan da take son yi.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5