Daga cikinsu akwai Aliyu Sani Madaki wanda ya ce, jam’iyyar APC ta zama mai raba kawunan ‘yan kasa sannan ba ta damu da hakkin dan adam ba kuma yana tsoron abinda zai biyo baya. "Idan ba a yi wasa ba sai dai rabewa," inji shi.
Madaki ya bayyana cewa sun shiga jam’iyyar ne domin kare hakkin al'umma da ba su tsaro, amma a halin da kasar take ciki babu daya da ake yi.
A bangaren Majalisar Dattawa kuma, a yanzu ta tabbata cewa Jam'iyyar APC ita dai ce ke ci gaba da rinjaye. Shugaban masu rinjaye Ahmed Ibrahim Lawan ya bai wa manema labarai wasu takardu mai dauke da jerin sunayen 'ya'yan jamiyyar da jihohin da suka fito. Jam'iyyar na da senatoci 53, PDP guda 50 , Jamiyyar ADC guda 3, APGA na da guda 2, sannan guda 2 kuma sun rasu.
Lawan yayi bayani cewa yana sa ran za a sake takaran wadannan kujerun biyu a watan Agusta mai kamawa, kuma da yardar Allah jam'iyyar APC ce za ta lashe kujerun.
To sai dai mai ba Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkar Majalisar Wakilai, Suleiman Kawu Sumaila, ya nuna alhininsa ga abinda ya faru da jam'iyyar APC, inda ya ce ba abune mai dadi ba, amma shi ya ga kokarin da Shugaba Buhari yayi a 'yan kwanakin nan domin ya hana 'ya'yan jamiyyar ficewa.
Kawu Sumaila ya ce siyasa tana tafiya ne da yawan mutane, idan ana raguwa ba alama ce mai kyau ba. Ya gargadin cewa a yi taka-tsantsan domin fada tsakanin manya bai cika haifar da alheri ba.
A wata takarda mai dauke da sa hannun kakakin gwamnatin tarayya Garba Shehu, ta nuna cewa Shugaba Buhari ya yi wa wadanda suka fita daga Jam'iyyar fatar alheri, tare da kira ga wadanda suka rage a jam'iyyar da su hada kai da shi wajen gyara Jam'iyyar saboda ta ci gaba da samun nasara.
Your browser doesn’t support HTML5