Har yanzu umurnin da Babban Bankin Najeriya ya bayar da ke cewa mutane na iya cire kudi naira dubu 100 duk mako, sannan kamfanoni suna iya cire Naira dubu 500 a mako, yana daukan hankalin wasu yan majalisar dattawan kuma sun nuna rashin jin dadi su, domin akan haka majalisar ta ba kwamitin kula da bankuna, inshora da hukumomin hada-hadar kudi umurni. In ji Sanata Adamu Bulkachuwa inda ya ce majalisa ta bada sharuda guda biyu.
Na daya, kwamitin kula da bankuna ya sa ido sosai kuma ya matsa wa Babban Bankin ya soke tsarin cire kudin, ko kuma ya kara yawan kudaden da za a cire. Bulkachuwa ya ce idan CBN bai bi shawarar su ba , to suna da 'yancin cewa akwai lauje cikin nadi a lamarin baki dayan sa.
Shi kuwa sanata mai wakiltan Sokoto ta Kudu Abdullahi Ibrahim Danbaba ya kalli tsarin ne ta wani bangare daban inda ya ce alamu na nuni da cewa ana so a musguna wa shirin zabe mai zuwa ne domin in an ce shi yana da 'yancin kashe Naira miliyan 100 wajen zabe, me ya sa za a bashi ka'idar kudin da zai cire a asusun sa.
Danbaba ya bada misali cewa a makonni 8 kenan zai ciro dubu dari 8 ne kawai, ina zai samu sauran abinda dokar zabe ta bashi daman kashewa.
Amma ga sanata Mohammed Adamu Aliero yana ganin tsarin cire kudin zai magance batun sayen kuri'u ko kashe kudi barkatai a daidai lokacin da zabe ke gabatowa a kasar.
Aliero ya ce yana goyon bayan tsarin cire kudin, domin zai hana 'yan siyasa yin facaka da kudi, kuma haka zai sa a zabi wadanda suka cancanta ne ba wadanda ke sayar da kuri'u ba, saboda haka za a tsaftace siyasar kasar ne baki daya.
Amma ga daraktan hada hadar kudi a Babban Bankin Najeriya CBN Ahmed Bello ya yi bayani cewa ba za a soke tsarin ba kuma ba za a yi kari akan yawan kudin da za a cire a mako ba, Bello ya ce ba a yi tsarin don a kuntata wa yan kasa ba, face don samun saukin hada-hadar kudi a kasar.
Majalisar dattawa ta ba kwamitin kula da bankuna, inshora da hada-hadar kudaden umurnin ya sa ido a tsarin cire kudin, in da hali a matsa wa bankin ya kara yawan kudin ko kuma wa'adin sauya kudin.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5