'Yan majalisar Amurka da hukumar kiwon lafiya na adawa da kashe kudin yakar cutar Ebola kan Zika

Majalisar dokokin Amurka

‘Yan majalisar dokokin Amurka da jami’an kiwon lafiya na kasa da kasa ko WHO, sun yi gargadi a kan janye kudin yaki da Ebola a maida shi kan yaki da kwayar cutar Zika, kwana daya bayanda gwamnatin shugaba Obama ta sanar da cewa tana shirin yin hakan.

Dan jam’iyar Democrat a majalisar dattijai, Ed Markey ya fada a wani zaman kwamitin harkokin kasashen ketare dake tattaunawa kan harkokin Afrika cewa, duk da yake an sami raguwar wadanda suke kamuwa da kwayar cutar Ebola, ba a shawo kan cutar ba tukuna. Kuma har yanzu yanayin da ya sa ta zama bala’i yana nan.

Sama da mutane dubu goma sha daya suka mutu da cutar Ebola a Afrika ta yamma cikin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu da kuma dubu biyu da goma sha biyar, abinda ya haifar da fargaba a fannin kiwon lafiya bayanda cutar ta bulla a Amurka da kuma Turai. Majalisar dokokin Amurka ta amince da kashe dala miliyan dubu dari da arba’in na gudanar aikin gaggawa, a yaki da cutar, wanda har yanzu ba a gama kashewa ba.

Ranar Laraba, Fadar White House ta sanar cewa, zata karkatar da kimanin dala miliyan dari shida da ya rage daga kudin yaki da cutar Ebola wajen yaki da kwayar cutar Zika da ta bulla. Cutar ta yadu cikin kankanin lokaci a kasashen kudancin Amurka, wadda ake dorawa alhakin haihuwar jarirai da mummunar nakasa.

Jami’an da suka bada bahasi a gaban kwamitin majalisar dokokin sunce wannan raguwar dabara ce.

Bakin ‘yan majalisa daga dukan jam’iyun yazo daya suna cewa, bai kamata a yi watsi da cutar Ebola ba domin har yanzu tana bullowa.