Shugabannin manyan kamfanonin fasaha na Amurka guda hudu – wato Apple, Amazon, Facebook, da Google - sun fuskanci tambayoyi daga 'yan majalisar dokokin Amurka a jiya Laraba, game da yadda suke amfani da karfin kasuwancinsu.
Babban shugaban kamfanin Amazon Jeff Bezos, ya kare ayyukan kasuwancin kamfaninsa da kuma kasuwar hannayen jarin kamfaninsa, inda ya fada wa kwamitin shari’a da kula da rashin yarda cewa, kashi 80 cikin dari na Amurkawa sun amince da kamfanin na Amazon baki daya."
Kwamitin ya dade yana bincike game da rashin yarda da kuma gasa ta hanyar manyan kwararrun kamfanin fasaha.
Bezos ya ce, "Yanzu kanana, da manya da matsakaitan ‘yan kasuwa 1.7 suna sayar da kayayyakin su a Amazon". "Amincewar da abokan cinikinmu suka yi da mu, ya saka a kullun suke baiwa Amazon damar kirkiro da wasu ayyukan yi a Amurka a cikin shekaru goma da suka gabata fiye da kowanne kamfani a kasar."