'Yan Majalisa Na Zargin Badakalar Kwangila

'Yan majalisa

Babban kotun jihar Adamawa ta dakatar da sassan biyu daga duk wani kuduri game da wannan batu, har sai an kammala sharia.

Wannan takaddamar dai ta biyo bayan wani zargi ne da wasu yan kwamitin raya karkara na majalisar dokokin jihar Adamawan suka yiwa kamfanin Hydro Resources sun hada baki da jami’an ma’aikatar raya karkara da wani kanin gwamnan jihar Alh. Abubakar Umaru Jibrilla wajen shakulatin bangaro a aikin kwangilar gyara wasu hanyoyin karkara a jihar a karkashin shirin bankin duniya na RAM-2, batun da yasa yan kwamitin gayyatar wadanda ake zargi a wani yanayi na kasa da awa guda da su bayyana gabansu.

Kuma kasa bayyanar wadanda ake zargin ne,a kasa da awa gudan sai yan majalisar suka fitar da sanarwar nemansu ruwa a jallo,tare da kuma da zargin badakalar sama da Naira biliyan daya a wannan kwangilar.

To ko me yasa ‘yan kwamitin ke wannan zargi da kuma dakatar da ayyukan da yan kwangilar suke yi ayanzu? Hon.Hassan Barguma shugaban masu rinjaye na majalisar kuma memba a cikin kwamitin yace sun dauki wannan mataki ne ganin yadda ‘yan kwangilar ke neman kwanciyar magirbi,inda basu aikin daya kamata.

To sai dai ko yayin da 'yan majalisar ke dakatar da ayyukan, tuni kamfanin Hydro Resources ta musanta zargin da ake yi,tare ma da garzayawa kotu don neman diyar Naira biliyan daya bisa abun da suka kira bata suna da suke zargin yan majalisar sun yi.

Alh.Maiwada Baba, daya daga cikin manyan daraktocin kamfanin yace abun mamaki ne zargin da yan majalisar ke yi ganin cewa basu fahimci yadda tsarin aikin na RAM ke tafiya ba,inda ko ya danganta lamarin da ce ce-ku cen da suka yi da wani dan majalisa.

Shima dai da yake maida martani,kanin gwamnan jihar Adamawan, Alh. Abubakar Umaru Jibrilla ya musanta zargin cewa kwangilar Naira biliyan biyu aka bashi.

Ko ma da menene dai yanzu Magana na gaban kotu inda mai sharia Nathan Musa, na babban kotun jihar ya bada umarnin dakatar da duk wani kuduri game da wannan batu,har sai an kammala sharia,da za’a soma ranar 14 ga wannan wata na Nuwamba.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisa Na Zargin Badakalar Kwangila - 3'49"