'Yan Luwadi Zasu Fuskanci Daurin-Rai-Da-Rai A Uganda.

Mutane a Uganda suke bayyana bakin cikinsu kan kisan wani dan kasar mai fafutukar kare 'yan luwadi kamarsa da aka kashe a 2011.


A Uganda majalisar dokokin kasar ta amince da wata doka wacce ta ayyana hukuncin daurin rai da rai kan ‘yan luwadi.
A baya dokar ta fuskanci suka daga kungiyoyin kare hakkin Bil’Adama da gwamnatocin kasashe dake yammacinduniya ciki harda Amurka saboda dokar ta kunshi hukuncin kisa.
Dokar da ta majalisar ta amince da ita jiya jumma’a bata kunshi sharidin hukuncin kisa ba, amma ta bukaci hukuncin daurin rai da rai kan abunda ta kira nau’I ko karfin wasu harkokin luwadi.
Wata jami’ar kungiyar rajin kare hakin Bil’Adama Human Rights Watch mai kula da shiyyar Afirka Maria Burnett tayi tur da sabuwar dokar duk da gyaran fuskar da aka yi mata. Haka ita ma Amnesty Intenational ta soki sabuwar dokar cewa tana nuna banabanci matuka.
Sai shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni ya sanya hanu kan kudurin kamin ta zama doka.