Jami’an dakarun SDF na Syria da Amurka ke goyon baya sun bayyana mamakinsu bayan da jami’an leken asirin Turkiyya suka kutsa wani sansanin ‘yan gudun hijira suka dauke wata mata ‘yar kasar Maldova da ‘yayanta guda hudu.
A ranar Juma’a 17 ga watan Yuli jami’an suka tabbatar da aukuwar lamarin da Turkiyya ta kitsa, wanda kafafen yada labaran Turkiyya suka fara bayyanawa, inda wata kafa ta ce bayan binciken farko da aka gudanar, ga dukkan alamu iyalin sun samu sun tsere ne bayan da suka boye a cikin wata motar daukar ruwa.
Amma jami’an sun ce ba a san takamaimai dalilin dauke iyalin ba.
Dakarun SDF na samar da tsaro ga sansanin al-Hol, wanda ke matsugunni ga dubban mata da yara da ke da alaka da ‘yan kungiyar IS. Dakarun da ke samun goyon bayan Amurka kuma suna kula da wani gidan yari a arewa maso gabashin Syria da ke dauke da mayakan IS 10,000.