Sanarwan na dauke da sa hannun mai Magana da yawun gwamnan jihar Kadunan Samuel Aruwan ya sanya wa hannu tace daga yanzu duk wani dan uwa musulmi mabiya mashabar Shia da aka kama yana tattaki akan hanya to zai huskanci daurin shekaru bakwai ko kuma hada masa duka biyu.
Samuel Aruwan yace wannan hukuncin da gwamnatin jihar Kadunan ta dauka akan ‘yan mashabar Shia bata sabawa dokokin kasa ba.
‘’Ranar 6 ga watan Oktoba na wannan shekarar da muke ciki majilisar zartarwa ta jihar Kaduna ta amince da shawarwari ko kuma matsayi wadda wannan kwamitin ta baiwa gwamnati, abinda ake nufi anan shine, daga ranar 7 jumaa ga watan oktoba cikin wannan shekarar da muke ciki na shekarar 2016 yanzu wannan kungiyar ta zama haramtaciyya a duk fadin jihar Kaduna domin ko basu da rajista bacin haka kuma akwai abubuwa wadanda suka shafi tsaro wadan da kwamitin tayi la’akari dasu ta kuma baiwa gwamnati wannan shawarar duk wani abu da gwamnatin jiha tayi, tayi ne abinda gwargwadon abinda dokokin kasa da kuma dokokin jihar Kaduna wadda ta bada hurumin ayi su’’.
Sai dai da wakilin muryar Amurka Isah Lawal Ikara ya tambayi mai Magana da yawun gwamnan cewa to ina matsayin sashen dokar kasa sashe na 38 dana 40 wanda ya baiwa mutane damar suyi kungiya ko kuma suyi harkokin sun a addini anan ko sai ya amsa da cewa.
‘’Wannan matsayar da gwamnatin jihar Kaduna ta fidda shi ba wai ya hana mutane yin addinin su bane, sai dai duk wani taro da wadannan mutanen zasu yi a karkashin wannan sunan da suke da ita an haramta ta a duk fadin jihar Kaduna, domin ko ma basu da rajista da gwamnatin tarayyar Najeriya ko kuma rajista da jihar Kaduna.
Ga Isah Lawal Ikara da Karin bayani 4’21
Your browser doesn’t support HTML5