Mai magana da yawun gwamnati a yankin Jowzjan Reza Ghafoori ya fadawa Muryar Amurka a yau Laraba cewa wannan hari ya auku ne a Gundumar Qurshtipa sannan maharan sun tafi da biyu daga cikin ma’aikatan na Red Cross.
Ya kuma ce ma’aikatan suna kan hanyarsu ta kaiwa manoma da iyalansu abincin dabbobi ne a gundumar yayin da tsagerun na Daesh suka far musu.
A wata rubutacciyar sanarwa da kungiyra ta Red Cross ta fitar, ta ce “sun girgiza kuma hankulansu sun tashi,” sun kuma tabbatar da cewa ma’aikatansu guda shida sun mutu sannan ba’a ga biyu ba a yankin na Jowzjan.
Tuni dai kungiyar ta Daesh ta dauki alhakakin kai wannan hari wanda aka kai shi a jiya Talata tare da bayyana sunan dan kunar bakin waken a matsayin Tajik.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 22 sannan ya jikkata 40 a Kabul din.