A Jamahuriyar Nijer jama’a na ci gaba da bayyana bacin ran su tare da gabatar da korafe-korafe dangane da matsalolin sadarwar da suke samu da wayoyin su na hannu wadanda ke karkashin gudanarwar kamfanonin kasashen waje masu zaman kansu.
Malam Abbas Abdoulazizi shi ne shugaban wata kungiya mai kare hakkokin masu yin amfani da wayoyin salula a kasar jamahuriyar Nijer:
Your browser doesn’t support HTML5
Daga cikin matsalolin da jama’ar ke kuka da su akwai rashin ingancin sadarwa, ga zare kudaden sadarwa ba tare da sanin mai kira ko mai layin waya ba, uwa uba kuma kamfanonin wayoyin kan kwashe kudade ko da mutum bai kira kowa ba, baicin duka wannan ga kuma matsalolin intanat a daukacin fadin kasar.
Babban jami'in gwamnatin kasar Nijer mai shiga tsakani da sasanta 'yan kasa mallam Cheffou Amadou ya ce zai kafa kwamitin da zai bi diddigi ya kuma gudanar da bincike akan wannan rikici. Shi ma babban jami'in kamfanin waya na Airtel ya ce ya na sane da koke-koken da jama'a ke yi kan irin matsalolin da suke fuskanta.
'Yan kasar Nijer dai na ci gaba da bayyana fushin su tare da yiwa kamfanonin wayar salula tofin Allah tsine da kuma bayyana su a zaman macuta, azzalumai masu yin shisshigi da katsalandan cikin harakokin kasar ta Nijer. Kuma 'yan Nijer din su na zargin kamfanin Orange da neman yin leken asiri ta hanyar yin amfani da wata na'urar da ta girka a kasar.
Kididdiga ta nuna cewa daga cikin 'yan kasar Nijer miliyan goma sha bakwai, mutane fiye da miliyan biyar ne ke yin amfani da wayoyin tafi da gidan na kamfanonin sadarwa hudu masu zaman kan su, uku na kasashen waje, daya kuma mallakin gwamnatin kasar Nijer