'Yan Kasar Nijer Sun Gaji da Gafara Sa Ba Su Ga Kaho Ba

Hoton inda kamfanin Areva ke hakar ma'adinin uranium a Arlit

'Yan kasar Nijer sun gaji da babakere da handamar kamfanin Areva na kasar Faransa mai hakar uranium a arewacin kasar
Jama'a sun yi tururuwa sun yi zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar jamahuriyar Nijer domin yin tir da Allah waddai da kamfanin Areva na kasar Faransa mai hakar ma'adinin uranium a arewacin kasar da kuma jan hankalin gwamnatin kasar Nijer kan yadda kamfanin na Areva ke cin karen shi ba babbaka, ya na handame arzikin kasa, ya na ci da gumin 'yan kasar, musamman ma masu sadaukar da kai su na yi mi shi aiki. Uwa uba kuma gwamnatin kasar Nijer na ci gaba da nuna halin ko oho da yadda kamfanin Areva ke gurbata yanayi, da kuma yadda tiririn dagwalon ma'adinin uranium ke jawowa ma'aikatan kamfanin da mazauna garin Arlit rashin lafiya. Ga rahoton da Abdoulaye Mamane Amadou y aiko daga Niamey babban birnin kasar jamahuriyar Nijer:

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga-zangar yin tir da gwamnatin kasar Nijer da kamfanin Faransa na Areva - 3:10