Daruruwan ‘yan Haiti sun yi zanga zanga a kan titunan Port-au-Prince a kwana na tara a jere zuwa jiya juma’a, dukkuwa da tabbacin da shugaban kasar ya bayar cewa yana sane da matsalolinsu yana kan daukan matakin warware su.
A ta bakinshi “muna kira da al’ummar duniya su taimakamana wajan kawar da shugaba Jevenel Moise, saboda Jobenel su ya kewa aiki” abinda wani mai zanga zanga ya fadawa sashen Creole na Muryar Amurka.
Ya kara da cewa “yan uwana ‘yan kasa, don Allah idan kunga Jovenel akan titi ku bugamar ankwa sannan ku jefashi kurkuku”.
Moise ya kawo karshen shiru da yayi na tsawon mako guda ta wajan jawabi da kasa da daren shekaran jiya Alhamis, wanda aka yada a kasa baki daya da kuma ta kafar sada zumunta ta Facebook. Ya yi kokarin kwantar da hankali da kuma bada tabbaci ma kasar dake cike da fushi.
Ata bakinsa “naji ku”, yana mai amsa zargin gazawa da akewa gwamnatin sa da kuma rashin gaskiya. Ya kara da cewa “bazan taba cin amanarku ba. Saboda ku nayi takarar shugaban kasa. Wa ku nake wa aiki.