'Yan Kasar Haiti fiye da dubu 50 zasu rasa kariyar ci gaba da zama a Amurka

Wasu 'yan Haitin da suka koma gida wannan shekarar

A shekarar 2010 sanadiyar wata muguwar girgizar kasa da ta auku a Haiti wadda kuma tayi raga-raga da kasar ya sa Amurka ta ba wasu 'yan Haitin kariyar zama a Amurka ta wucin gadi to amma yanzu da kasar ta fara farfadowa Amurka ba zata sabunta kariyar ba da zara wa'adinta ya kare

Bayan kwashe shekaru masu yawa ana kare ‘yan kasar Haiti daga mayar da su kasarsu, yayin da Haiti ke ci gaba da farfadowa daga mumunar girgizar kasar da ta afka wa kasar a shekara ta 2010, dubban ‘yan Haitin zasu rasa kariyar wucin gadin da take kare su.

Kariya ko kuma matsayin wucin gadin da ake baiwa yan gudun hijirar da suka cancanta da ake kira TPS a takaice, zata daina aiki ga akalla ‘yan kasar Haiti dubu 50 dake zaune suna aiki anan Amurka.

A lokacinda suke bada wannan sanarwar, Jami’an sunce yanayin kariyar wucin gadin wadda aka tanadar dalilin girgizar kasar da ta afkawa Haiti a shekarar 2010, yanzu an soke ta.

Amma masu raji na ikirarin cewa kasar Haiti ba zata iya ‘daukar nauyin mutanen da za a mayar kasar ba, bayanshekaru bakwai da faruwar girgizar kasa mai nauyin maki bakwai, wadda ta haddasa asarar Biliyoyin daloli, ta kuma yi sanadiyar rasa rayukan mutane dubu 300 da raunata wasu kimanin miliyan ‘daya da dubu dari biyar, adadin dake zama daidai da yawan mutanen da suka rasa muhallinsu.