‘Yan Kasar Chadi Dake Niger Suna Jefa Kuriar Zaben Shugaban Kasa Da Ake yi A Kasar Su.

  • Ladan Ayawa

Mazabar "Tarauni Gardens" a Kano ana tantance sunayen masu zabe kafin su fara jefa kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin tarayya

Daga cikin’yan chadi miliyan 6 dake rubuce cikin kundin rajistan zaben kasar kimanin 200 ne suka yi rajista a jamhuriyar Niger.

Wannan yasa wadannan mutanen yau suka hallara a daya daga cikin runfar zaben da aka bude a ofishin kasar Chadi dake kasar Yamai.

Jakadar na kasar ta Chadi Muhammadu Nuru Malaige shine ya kaddamar da wannan zaben kuma ga abinda yake cewa cikin harshen Faransanci.

‘’Yace yana farin jefa kuriar sa kamar yadda abin yake wajen sauran ‘yan kasa da suke ciki da wajen kasar wadanda a yau zasu halarci runfunar zabe domin kada nasu kuriu kumaina fata ayi wannan zaben cikin kwanciyar hankali da cikakken tsaro.’’

Ga Sule Mummuni Barma da ci gaban labarin 2’27

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Kasar Chadi Dake Niger Suna Jefa Kuriar Zaben Shugaban Kasa Da Ake yi A Kasar Su. 2'27