'Yan Kasar Burundi Suna Zaben Shugaban Kasa

Burundi

Sama da masu zabe miliyan 5 ne, suka fito kada kuri’a a Burundi da ke gabashin Afirka domin zaben sabon shugaban da zai gaji daddaden shugaban kasar Pierre Nkurunziza.

Nkurunziza zai sauka daga mulkin kasar bayan kwashe shekaru 15 akan wannan kujera inda shekaru 5 na karshe suka kasance tattare da tashe-tashen hankula, bayan da yayi yunkurin zarcewa a wa’adi na 3, abin da ya tursasawa sama da ‘yan kasar 300,000 arcewa daga kasar mai fama da talauci.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana da cewa, dakarun gwamnati sun auna daruruwan mutanen da aka kashe a lokacin rikicin, zargin da Burundi ta musanta.

‘Yan takara 7 ne suke fafatawa a zaben na wanda zai gaji Nkurunziza, ciki har da tsohon janar din kasar Evarist Ndayishimiye, da kuma babban shugaban adawa Agathon Rwasa.

Ana kuma gudanar da zaben na yau a yayin da Burundi ke fama da barkewar annobar coronavirus, inda take da mutane 24 da suke da cutar da mutuwar mutum daya tilo daga cikin ‘yan kasar da ke da yawan mutane miliyan 11.