'Yan Kano Sun Maida Martani Kan Matakin Takaita Zirga Zirgar Baburan A Daidaita Sahu

Baburan A Daidaita Sahu a Kano (AP)

Yayin da masu sana’ar tuka babura masu kafa 3 da aka fi sani da A daidaita sahu a Kano da fasinjoji ke mayar da martani game da matakin gwamnatin jihar na takaita zirga zirgar baburan daga karfe shida na safe zuwa karfe goma na dare, gwamnatin ta yi karin haske dangane da wuraren da dokar ta shafa.

KANO, NIGERIA - A cikin wata sanarwar gwamnati da kwamishinan yada labarai Mohammed Garba ya sanya wa hannu, ta ce daga yanzu gwamnatin jihar ta haramta zirga zirgar baburan A daidaita sahu a dukkanin fadin jihar bayan karfe goma na dare, a don haka masu wadannan babura na da izinin zirga zirga daga karfe shida na safiya zuwa karfe goman dare.

Sanarwar ta ce duk wanda aka kama yana sana'ar a lokutan da gwamnati ta haramta babu shakka jami’an tsaro zasu dauki mataki akansa.

Mohammed Garba ya ce dalilan wannan doka shi ne gwamnati ta yi la'akari da abubuwan da ke faruwa musamman ta fannin tsaro, shi ya sa majalisar tsaro ta jihar ta bada shawarar a dauki matakin gaggawa.

Sai dai ga alama wannan mataki na gwamnati ya zo da damuwa ga masu amfani da wadannan babura na A daidaita sahu wajen zirga zirgar su ta yau da kullum, suna cewa akwai takura ga marasa abun hawa.

Kazalika su ma matuka baburan na A daidaita sahu sun koka kan matakin tare da yin kira ga gwmanati da ta duba lamarin.

To amma Mohammed Garba ya ce idan ba cikakken tsaro a jihar su kansu 'yan A daidaita sahun ba zasu iya yin sana'ar ba.

Masana kididdiga sun yi hasashen cewa baburan A daidaita sahu da ke zirga zirga a birni da kewayen Kano sun tasamma miliyan guda, kuma galibin al’uma sun dogara da su wajen zirga zirgar yau da kullum.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Kano Sun Maida Martani Kan Matakin Takaita Zirga Zirgar Baburan A Daidaita Sahu