Umurnin tsaftace muhallin 'yan Ogoni da shugaba Muhammad Buhari ya bayar ya sa masu ruwa da tsaki sun fara yunkuri saboda tabbatar da aikin ya gudana.
Aikin da za'a fara zai dauki shekaru talatin cur kafin a kammalashi.
Wannan matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na gyara muhallin al'ummar Ogoni wadda ta dade tana fama da gurbatacen muhalli ya sa 'yan yankin sun fara mayar da martani.
Wani Mr. Kiki dan yankin yana cewa mu mutanen Ogoni muna cike da murna matuka domin mun dade muna kururuwar neman hakan. Abun farin ciki nan ko dan yankinmu da ya yi shugaban kasa ya kasa tabuka komi a kan lamarin. Saboda haka muna murna da gwamnatin Muhammad Buhari.
Shi kuma wani yace dole ne ya yabawa shugaba Buhari akan wannan aiki da ya bada umurnin a yishi saboda rahoton Majalisar Dinkin Duniya akan muhallin yankin Ogoni ya dade yana yawo. Matakin da shugaban ya dauka tamakar cika alkawarin da ya ne lokacin da yake neman shugabancin kasar.
Mr. Sobari yace gyara muhallin yankinmu abun marhaban ne. Wani kuma yace matakin babban al'amari ne da zai sauya rayuwar mutanen yankin da ma yankin Niger Delta baki daya.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5