'Yan Jaridar Sudan Sun Fara Yajin Aiki, Da Goyon Bayan 'Yan-Adawa

Wasu ‘yan jaridar kasar Sudan sun tsunduma cikin yajin aiki, don nuna goyon bayansu ga zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.

Yajin aikin na kwanaki uku da kungiyar ‘yan jaridar Sudan ta sanar yau Alhamis, shi ne mataki na baya-baya cikin jerin zanga-zanga a lokuta daban-daban, da aka fara yi a fadin kasar tun ranar 19 ga watan nan na Disamba, saboda karancin man fetur, abinci da kuma matsanancin karuwar farashin Buredi.

A karon farko cikin mako guda, ba a samu rahoton wata sabuwar zanga-zanga ba a Sudan gashi yau Alhamis. Masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa da ke birnin Khartoum shekaran jiya Talata, suna neman shugaba Bashir ya yi murabus daga mukaminsa.

Bashir ya yi tir da masu zanga-zangar, inda ya kwatantasu a matsayin “maciya amanar kasa,” kuma “sojan haya” amma shugaban ya yi alkawarin daukar matakan yin garambawul ga tattalin arzikin kasar.

Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International a ranar Talata ta ce, tana da “sahihan rahotanni” da suka nuna cewa dakarun gwamnati sun kashe masu zanga-zanga 37 a makon da ya gabata, ta kuma zargi gwamnatin da yin amfani da karfin da ya wuce kima akan masu zanga-zangar da ba sa dauke da makamai.