‘Yan Jarida Su Jajirce Wajen Gudanar Da Aikinsu Ba Tare Da Fargaba Ba

Jarida.

An karfafawa ‘yan jarida gwiwa kan su jajirce wajen gudanar da aikinsu ba tare da fargaba ba.

An gudanar da wani taron bita da kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Filato ta shirya don tunawa da wasu ‘ya ‘yan ta takwas da suka rasu a bakin aiki shekaru goma da suka gabata.

Mai gabatar da kasida a wajen taron kuma babban darakta a gidauniyar horas da ayyukan masana’antu ta ‘kasa Joseph Ari, ya ce ‘yan Jarida na fadawa hadari da dama lokacin da suke gudanar da aikinsu.

Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta ‘kasa reshen jihar Filato Yakubu Tadi, yace kungiyar ta shirya wani tsari na tantance jabun ‘yan jarida don tsabtace aikin jarida a Najeriya.

Mai martaba sarkin Wase, Alhaji Mohammadu Sambo Haruna, wanda Galadiman Wase Alhaji Mustapha Umar ya wakilta, ya shawarci ‘yan jarida da su rika tantance labari kafin su yada.

Domin sauraren cikakken labarin saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Jarida Su Jajirce Wajen Gudanar Da Aikinsu Ba Tare Da Fargaba Ba - 3'44"