'Yan Jarida a Rasha Sun Rubuta Takardar Koke Bayan Da Aka Kama Dan Uwansu

Dan jarida Ivan Safronov

'Yan jarida a kasar Rasha sun rubuta takardar koke ta bukatar a bayyana zarge-zargen cin amanar kasa da ake yi wa dan jarida Ivan Safronov, saboda ganin da suke cewa zargin kage ne yayin da ake dada taushe 'yancin 'yan jarida.

An kama wani tsohon dan jaridar kasar wanda ke aiki yanzu a hukumar nazarin sararin saman kasar, kuma ana tuhumarsa da cin amanar kasa saboda zargin tura wa Yammacin duniya bayanai, wanda hakan, a cewar magoya bayansa, wani bita da kulli ne saboda yadda ya yada labaransa game da sojoji da kuma siyasar kasar.

Ivan Safronov

Ivan Safronov dan shekaru 30, ya shafe gomman shekaru da su ka gabata ya na aikin jarida na yada labarai game da soji a kafafen labaran Kommersant da Vedomosti, wadanda wasu manyan jaridu ne a kasar da tasirinmu ya yi ta raguwa saboda rage muhimman ma’aikata, yayin da su ka yi ta fuskantar matsaloli masu nasaba da kokarin tauye ‘yancin jarida a Rasha.

Hoton bidiyon da Hukumar Harkokin Tsaron Tarayya ta fitar, na nuna yadda aka kama tsohon dan jaridar, yayin da ya doshi motarsa a harabar gidansa a birnin Moscow da safiyar ranar Laraba.