Jami’an kasar Yemen sun ce ‘yan tawayen kungiyar Houthi ta ‘yan Shia’ da abokan kawancensu sun yi ta bude wuta har suka sami kutsawa tsakiyar Aden jiya Alhamis suka kwace fadar shugaban kasa a birnin mai tashar sufurin jiragen ruwa.
‘Yan tawayen sun yi ta kutsawa cikin Aden ‘yan kwanakin nan, yayinda gumurzun ya tilastawa dakarun shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi dake da goyon bayan kasashen ketare, arcewa daga Aden makon da ya gabata.
Kwace Aden da suka yi, birni karshe da ya rage a hannun dakarun dake goyon bayan Mr Hadi, ya zama wata koma baya ga rundunar hadin guiwa da kasar Saudi Arebiya ke jagoranta, wadda ta shafe sama da mako guda tana kai hare hare ta sama a Yemen
A wani taron manema labarai a Riyadh babban birnin kasar Saudiya, wani jami’in tsaron kasar yace ya hakikanta cewa, kawo yanzu, kura ta lafa a birnin.