Jam'iyun Hamayya Suna Ci Gaba Da Zaman Dirshan Kan Haraji A Kasafin Kudin Bana.

Hagu zuwa Dama: Sakataren Hukumar raya Tabkin chadi, Sanusi I. Abdullahi; Shugaba Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin; shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya; shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar; shugaba Idris Deby na Chadi; wakilin shugaban Kamaru, minist

Jam'iyun suka ce babu gudu babu jada baya, domin akwai alamun gwamnati ta yi kunnen kashi kan koken jama'a.

A jamhuriyar Nijar, wasu jam’iyun siyasa na kawancen adawa masu zaman kansu na can na ci gaba da zaman dirshan a dandalin TUMO dake birnin yamai a wani sabon salon gwagwarmayar da suka bullo da shi, don tilastawa hukumomin kasar su aiwatarda gyaran huska akan tsarin kasafin 2018 da suke zargin yana kunshe da harajin dake jefa talakawa cikin halin tsadar rayuwa yayinda gwamnatin ta NIJER ke cewa ba haka zancen yake ba.

Wakilinmu Sule Mumini Barma ya tantauna da jagorar wadanan jam’iyu Hajiya Maryama Gamace, ta koka kan abunda ta kira "kunnen kashi" da gwamnatin kasar ta dauka, domin ita gwamnatin bata mutunta zanga zanga da jerin gwano da al'umar kasar suke tayi da zummar jawo hankalinta kan halin kunci da kasafin kudi na 2018 zai kara jefa al'umar kasar ba.

Gameda tsawon wannan zaman Hajiya Maryama tace muddin jama'a suna nan za su ci gaba da zama sai baba ta gani.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaman dirshan a Yamai