'Yan Gudun Hijirar Kamaru Sama Da 35,000 Suka Je Najeriya

Najeriya kamar kasashen da take makwabtaka da su a nahiyar Afika ita ma tana fama da matsalar ‘yan gudun hijira daga gida da waje.

Dubban ‘yan kasar Kamaru da suka tsere daga kasar saboda tashin hankalin siyasa yanzu suna Najeriya. Hukumomin Najeriya sun ce ‘yan gudun hijira fiye da dubu talatin da biyar suka isa kasar tun daga shekarar 2016, amma ‘yan rajin kare hakkokin ‘yan gudun hijira sun ce adadin ya zarta haka, ya ma wuce dubu saba’in. A yayinda kasashen duniya ke tunawa da ‘yan gudun hijira a yau 20 ga watan Yuni, hukumomin Najeriya sun ce zasu fara maida ‘yan gudun hijirar Kamaru dake so su koma kasashen su.

Ernest Cho dan kasuwa ne a Kamaru kafin ya tsere daga kasar da ‘yayan sa maza biyu zuwa Najeriya.

Cho na daya daga cikin ‘yan kasar Kamaru dubu dari hudu da talatin da bakwai da akan tilas suka gujewa kasarsu sakamakon tashin hankalin dake faruwa a yankunan kudu maso yammacin kasar da arewa maso yammacin kasar.

Yanzu yana babban birnin Najeriya wato Abuja, inda yake kokarin fara rayuwa.

Cho ya ce gidansa dake kauyensu, kusan babu wanda ke zama cikin sa. Kowa ya tsere.