'Yan gudun Hijirar Boko Haram Sun Fara Numfasawa A Borno

Your browser doesn’t support HTML5

Miliyoyin mutane rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da wasu yankunan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya a cewar hukukomi.
Sannu a hankali dai, ‘yan gudun hijirar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya suna samun agaji domin saukake mawuyacin hali da suke ciki. Hukumar Raya Arewa Maso gabashin kasar ta mikawa gwamnatin jihar Borno gidaje dubu daya domin rabawa ‘yan gudun hijira. Hukumar ta kuma horas da matasa sana’o’i domin dogaro da kansu. Hussaina Mohammed na dauke da rahoton daga Maiduguri.