Yan Gudun Hijiran Rohigya Suna Fama da Raunin Jiki, Inji Majalisar Dinkin Duniya

Yan Gudun Hijiran Rohingya

Wani binciken da hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD ta gudanar tsakanin yan gudun hijiran kabilar Rohingya da suke zaune a Bangladesh da yawansu ya haura rabin miliyon, ya nuna kashi daya cikin uku masu rauni ne kuma suna bukatar taimako na musamman.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da yan gudun hijiran Rohingya dubu dari shida ne suka isa Bangladesh daga Myanmar tun ranar 25 ga watan Agusta.

An gudanar da wannan binciken ne a sansanin Kutupalong da matsugunan yan gudun hijiran na wucin gadi da kuma wuraren duban lafiyarsu a Cox’s Bazar. Hukumar yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hukumar bada agaji ta Bangladesh ne suke yi hadin gwiwa wurin gudanar da binciken.

Hukumar yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane dari aka dauka suna shiga wuraren kwanan yan gudun hijira suka tattara bayanan iayalai sama da dubu dari da ashirin da yawansu ya kusa dabu dari biyar da goma sha takwas. Kakakin hukumar yan gudun hijiran ta MDD Duniya Aslam Khan tace akasarin wadanda suka fara isa Bangladesh mata ne da yara.

Your browser doesn’t support HTML5

ROHINGYA SURVEY