Wannan ma kuwa na zuwa ne yayin da hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA, kema kai wasu kayakin tallafi ga yan Najeriyan dake gudun hijira a Kamaru sakamakon rikicin na Boko Haram,wanda yayi sanadiyar asarar dubban rayuka a Najeriya da wasu kasashen dake makwabtaka da ita.
Hukumar dai ta NEMA, tace yanzu haka yan Najeriyan dake makale a kasashen ketaren na son komowa gida,kasancewar hankula sun soma kwantawa a yankunansu.
Sani Datti dake zama jami’in hulda da jama’a na hukumar NEMA a Najeriya,yace yanzu haka yan Najeriyan na son komowa gida Najeriya.
Kamar dai hukumar NEMA, ita ma hukumar dake da alhakin kula da yan gudun hijira ta Najeriya,wato National Commission For Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons (NCRMI) tuni ta soma zagayawa jihohi ukun nan da rikicin Boko Haram yafi shafa,jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe don ganin halin da yan gudun hijira ke ciki.
A ziyarar kawo kayan tallafi da tawagar hukumar suka kawo jihar Adamawa,babbar kwamishiniyar hukumar Hajiya Sadiya Umar Faruk tace,hukumar a yanzu zata maida hankali ne wajen sake tsugunar da yan gudun hijiran.
Shima da yake jawabi yayin raba kayakin tallafin gwamnan jihar Adamawa,Sen.Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla ya yaba da nasarorin da ake samu yanzu a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.
Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram ya tilastawa gudun hijira,zuwa kasashen waje baya ga wadanda yanzu ke sansanonin da aka tanadar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5