Sakamakon wani binciken da wasu hukumomin Majilisar Dinkin Duniya suka yi,sun gano ‘yan gudun hijirar kasar Syria dake zaune a Lebanon suna zama cikin mawuyacin hali.
Hukumomi da suka gudanar da wannan bincike sun hada da hukumar kula da ‘yan gudun hijira,dana kula da asusun tallafawa yara, sai kuma hukumar kula da shirin samar da abinci. Sunce sun gano cewa ‘yan gudun hijirar kasar Syria da yawan su yakai sama da miliyan guda dake zauna a kasar ta Lebanon suna rayuwa ne akan kasa da dala 4 a rana.
Wakiliyar wannan gidan radiyon Lisa Schlein a cikin rahoton ta tace bayan shekaru da akayi ana yaki, binciken da MDD ta gudanar game da ‘yan kasar ta Syria dake gudun hijira a kasar Lebanon an gano kusan kullun sai kara talaucewa suke yi.
Tace harma abinda zasu ciya fara zama musu jan aiki.
Har ila yau kuma binciken ya nuna cewa a kowane gida ana kashe a kalla kusan dala 98, amma kusan rabin sa yana tafiya ne wurin sayen abinci.
Binciken na wadannan hukumomin na MDD ya nuna cewa ‘yan gudun hijirar suna rancen kudi dominsu sayi abinci, su biya bukatun su na kiwon lafiya kana su biya kudin haya.
Wannan yasa a kalla cikin ko wasu yan gudun hijira 10 tara daga cikin su suna bugewa ne ga cin bashi kafin su samu dan walwala.
Wannan yasa mai Magana da yawun hukumar kula da Yan gudunhijira na MDD William Spindler yace wannan yasa ‘yan gudun hijra suka zama kamar wani hadari.
Haka kuma samun damar zama bisa doka ga ‘yan gudun hijirar ya zame wani alkakai, abinda yasa da dama daga cikin su suke fuskantan hadarin kamewa daga hukumomi.
Wannan halin oni ‘yasun dasuka suka samu kansu ciki yasa da yawan su basu samun aikin yi balle,aika yaran su makaranta ko kuma samun kula da lafiyar su.
Spindler ta fada wa muryar Amurka cewa wannan halin kunci yasa da yawan su fadawa cikin miyagun ayyuka, harma da yiwa ‘ya’yan su mata aure da wuri.