'Yan gudun hijira sun zargi jami'an Kamaru da cin mutuncinsu

'Yan gudun hijira da Kamaru ke tura keyarsu zuwa gida Najeriya

'Yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya tilasta masu arcewa Kamaru sun koka da irin cin mutuncin da jami'an kasar suka yi masu

'Yan Najeriya 'yan gudun hijira da aka taso keyarsu zuwa jihar Adamawa sun koka da cin mutuncin da suka ce kasar Kamaru tayi masu kafin ta tasa keyarsu zuwa Adamawa.

Mutanen sun zargi kasar Kamaru da kulle wasunsu a gidan kaso da kuma kwace masu kadarorinsu kafin kasar ta tasa keyarsu zuwa jihar Adamawa dake makwaftaka da kasar.

Wata mata tace mijinta aka kama aka kulle ba tare da aikata wani laifi ba kana aka kwashesu zuwa Adamawa amma ita daga Maiduguri take. Akwai wasu ma da suka ce an ci zarafinsu da kuma gallaza masu azaba a hannun hukumomin kasar Kamaru.

Wani Alhaji Mustapha daga Gamboru Ngala dake jihar Borno yace yayinda suke Kamaru an gana masu azaba.

Malam Bello Sa'ad shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa ya bayyana matakan matakan da suka dauka na kare hakin 'yan gudun hijiran. Yace batun kayansu da aka kwace sun mikawa hukumomin da suka kamata su kwato masu.

Yanzu 'yan gudun hijiran sun mika kokensu ga hukumar kare hakin dan Adam ta shiga lamarin.

Sanasanonin 'yan gudun hijra a Adamawa na cigaba da karbar 'yan gudun hijiran dake kwararowa daga Kamaru.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan gudun hijira sun zargi jami'an Kamaru da cin mutuncinsu - 2' 44"