'Yan Gudun Hijira Sun Samu Sa'ida a Abuja

Wata Kungiyar Jinkai a Najeriya, Mai suna LIKEMINDS PROJECT, tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi biyu a ciki da wajen Najeriya, sun tallafawa wasu ‘yan gudun hijira, da tarzomar Boko Haram, y araba da gidajensu da a halin yanzu ke samun mafaka a kauyen Wasa dake Abuja.

Shugabar kungiyar ta kasa Hajiya Fatima Kyari Muhammad, ta bayyana cewar kungiyar tasu tayi hadin gwiwar da wasu kungiyoyi biyu,wato kungiyar dake tallafawa wadanda tarzoma ta raba da gidajensu, da kuma wace ke karfafar tattalin ‘yan gudun hijira mai cibiya a birnin London.

Yayin da a wannan karo suka fi maida hankalinsu bisa ga wadanda tarzomar Boko Haram ta raba da gidajensu, a inda suka kai kayayyakin jinkai ga irin wadannan mutane dake samun mafaka a kauyen wasa a Abuja babbab birnin Najeriya.