Dubban Yan Gudun hijirar dake zaune a sansanin da ake kira Bakasi dake cikin garin Maiduguri suka koka game da rashin samun abinci daga watanni biyu zuwa ukku. Suka ce gwamnati bata waiwayo su ba kamar yadda aka saba musu duk wata.
WASHINGTON DC —
Wadannan ‘yan gudun hijiran sun fito ne daga kananan hukumomin kusan guda 5 dake samun mafaka a wannan sansanin na Bakasi wanda har wannan al’ammari ya nemi tada hankalin ‘yan gudun hijira.
Ganin cewa gwamnatin ce ke tallafa musu da abinda zasu ci hakan yasa wasun su ma fita zuwa yawon bara, wasu kuma fita neman ayyukan da zasu yi domin dai abinda zasu sa a baka, da yake mafi yawan su suna tattare da iyalan su.
Ga abinda wau daga ikin su ke cewa.
‘’Mu munkai shekaru 3 a cikin wannan wurin’’
A gaskiya mun samu canjin yanayi a yanzu, alhamdulillahi muna dan samun.
To amma kuma sunce kamar watanni 3 kenan ba a bamu abinci ba a cikin wannan wurin.
Ga Haruna Dauda da Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5